An Fara Shari\’ar Mabiyan Sheikh Zakzaky A Gidan Yari

0
2453

Rabo Haladu, Daga Kaduna.

AN  soma shari\’ar \’yan kungiyar Shi\’a da ake zargi da hannu a rikicin da ya barke kwanaki a tsakanin \’yan
kungiyar da sojoji a Zariya.
\’Yan Shi\’a kusan 200 aka gabatar ga kotun da ta zauna a cikin gidan yarin Kaduna domin tsaro. An dai bayar da belin mutane hudu daga cikin wadanda ake zargin.
Idan ba a manta ba,  cikin watan Disambar bara ne, aka yi tashin hankali tsakanin \’yan Shi\’a da sojoji lamarin da ya janyo rasuwar mutane da dama tare da tsare shugaban kungiyar, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.
Haka kuma tuni gwamna Nasir Ahmed El-Rufai ya rantsar da kwamitin shari\’a domin binciko musabbabin rikicin da ya faru a tsakanin sojojin da \’yan mazhabar Shi\’a.
Gwamnatin jihar Kaduna ta kafa kwamitin mai wakilai 13 ne a karkashin jagorancin wani babban alkali na kotun daukaka kara ta tarayya, Mai shari\’a Mohammed Lawan Garba, domin tantance gaskiyar  lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here