Kwale-kwale Ya Nutse Da Fasinjoji Cikin Kogi A Jigawa

0
985

Rabo Haladu Daga Kaduna
RAHOTANNI daga karamar hukumar Jahun a jihar Jigawa na cewa wasu mutane da dama sun rasa ransu
sakamakon kifewar da kwale-kwalen su ya yi a cikin wani kogi a yankin.
Kawo yanzu dai an gano gawar mutane takwas, yayin da ake kuma ci gaba da neman wasu mutanen da dama da suka nutse a cikin kogin.
Shugaban karamar hukumar Jahun, Alhaji Umaru Muazu ya shaida wa manema labarai  cewa kawo yanzu ba za a iya tantance adadin mutanen da lamarin ya rutsa da su ba, har sai mutanen da aka ceto sun koma gida, sannan a iya tantance mutane nawa ne ba a gani ba. Kawo yanzu dai ana ci gaba da aikin laluben mutanen da ake zaton sun nutse a kogin. Shugaban karamar hukumar ta Jahun ya ce mazauna yankin ba su da wata hanyar sufuri sai ta amfani da kwale-kwale.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here