Yan Sanda Sun Kama Buhunan Tabar Wiwi 33, Kwandunan Miyagun Magani 34 A Kaduna

0
1596

IMRANA ABDULLAHI Daga Kaduna

A KOKARIN ganin an tsaftace Jahar Kaduna daga miyagu da sauran bata garin da ke kawo cikas ga zaman lafiya ya sa jami\’an tsaron rundunar tsaron \’yan sanda karkashin Umar Shehu, ta gunadar da yin wata sharar kame duk masu sayar da miyagun kayan maye a cikin garin Kaduna kawai.

Sakamakon yunkurin na cikin garin Kaduna ya haifar wa da rundunar nasarar kame wata dalar buhunan tabar wiwi 33 da kuma kwandunan sayar da kayan maye 34 a cikin garin Kaduna kawai.

Kwamishinan \’yan sanda Umar Shehu, a lokacin da yake gabatar da wadannan kayan da aka kama gaban manema labarai ya ce sun yi nasarar kame wadanda ake zargi da suka kai mutane 150 da a halin yanzu suke gaban kotuna domin yi masu shari\’a.

 

 

 

\"Kwandunan

Kwamishinan ya kuma ce sun kame wadansu kayan maye da suka hada da Tabar wiwi buhuna 10 a cikin buhunan Bako, sai kuma katan 10 na miyagun kwayoyi da kuma Jarkoki 17 na kayan maye na ruwa da ake sayar wa jama\’a.

Kwamishinan \’yan sanda Umar Shehu, ya kuma yi godiya ga gwamnan Jahar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufa\’i bisa goyon baya da kuma hadin kan da yake ba rundunar da yake yi wa jagoranci.

 

 

\"Gangar

Musamman bisa yadda Gwamnan ya wuce gaba wajen fadakarwa a kan miyagun kwayoyi,wanda hakan kuma ya haifar da samun nasara wanda kuna gani mun samu wannan nasara ne a cikin garin Kaduna kawai don haka za mu ci gaba ta yadda za mu yi nasarar raba al\’umma da matsalar masu shaye-shaye da kuma masu sayar da kayan maye.

 

 

 

\"Tabar

Kamar yadda jama\’a suka sani ne miyagun kwayoyi na yin jagoranci wajen haifar da laififfuka da dama a cikin al\’umma da suka hada da fyade da sauransu.

Ya kuma yi bayanin cewa za su hannanta dukkan wadannan kayayyakin da suka kama ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa wato (NDLEA).

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here