Rusau A Dan-Bushiya: Manema Labarai Sun Sha Da Kyar

0
1743

Imrana Abdullahi, Daga Kaduna
MANEMA labarai sun sha da kyar a hannun matasan da suke cike da fushi a unguwar Dan-Bushiya fa aka fi sani da \’Millennium city\’ a cikin garin Kaduna.

Al\’amarin na sha da kyar da manema labarai suka yi,  ya faru ne sakamakon matsalar da aka samu tsakanin matasa mazaunan unguwar Dan-Bushiya ne a yayin da tawagar jami\’an tsaro da kuma ma\’aikatan hukumar tsara birane ta Jahar Kaduna suka sauka a unguwar domin rusa wani wurin da aka yi gini ba bisa ka\’ida ba kamar yadda dokar tsara birane ta shimfida.

Idan dai za a iya tunawa Gwamnan Jahar Kaduna mai ci a yanzu, ya tabbatar wa da duniya cewa gwamnatinsa za ta dawo da filayenta da \’yan share-wuri-zauna suka mamaye.

Su dai mutanen Dan-Bushiya sun sauka a kan manema labarai ne a lokacin da ma\’aikatan hukumar tsara birane tare da tawagar motocin jami\’an tsaro suke rushe wuraren da wasu suka yi gini ba bisa ka\’ida ba, inda ,su matasan suka dauka cewa, su ma manema labarai suna cikin tawagar jami\’an tsaro ne ko kuma ta ma\’aikatan hukumar tsara birane.

Saboda kokarin hucewar da mutanen Dan-Bushiyar suka yi ya sa manema labarai sha da kyar ta hangar kafa me na ci ban ba ki ba.

Kokarin wakilinmu na jin ta bakin masu magana da yawun hukumar KASUPDA ko kuma jami\’an gwamnati lamarin ya ci tura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here