An rantsar da Ali Modu Sheriff Sabon Shugaban Jam\’ iyar PDP na kasa.

  0
  1299

   

  Rabo  Haladu Daga Kaduna

  AN rantsar da tsohon gwamnan Jihar Borno Sanata Ali Modu Sheriff, a matsayin sabon shugaban  jam\’iyyar adawa ta PDP a jiya ranar Litinin.
  Sheriff, wanda ya koma jam\’iyyar daga jam\’iyyar APC ya karbi ragamar shugabancinta ne daga Prince Uche Secondus, a wajen wani takaitaccen biki da aka gudanar a hedikwatar jam\’iyyar da ke
  Abuja.
  SAS, kamar yadda ake yi masa lakabi, ya karbi shugabancin jam\’iyyar ne bayan da majalisar zartarwar jam\’iyyar ta zabe shi a zaman shugabanta a ranar Talatar makon da ya gabata.
  Sai dai wasu manyan shugabannin jam\’iyyar sun nuna matukar adawa da zaben nasa.
  A ranar Lahadi ma wata kungiyar wasu kusoshin jam\’iyyar da ake kira PDP Rescue Group, ta yi kira ga Ali Sharif da ya yi murabus.
  A cikin jawabinsa ya yi alkawarin sake mayar da jam\’iyyar kan turba da kuma mayar da ita jam\’iyyar da talakawa za su dinga jujjuya al\’amurranta.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here