MTN Ta Fara Biyan Tarar Dala Miliyan 250 Ga Gwamnati

  0
  1071

  Rabo Haladu Daga Kaduna

  KAMFANIN sadarwa na MTN ya sanar da fara biyan tarar dala miliyan 250 ga hukumar sadarwa ta Nijeriya, a matsayin wani bangare na tarar da aka dora masa.
  A wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Laraba, ya ce, kamfanin ya kuma janye karar da ya shigar da gwamnatin kan dora masa tarar kusan Dala Biliyan ($3.9).
  Hukumar sadarwa ta Najeriya ce dai ta dora wa MTN tarar bisa samun kamfanin da laifin kin katse layukan mutane miliyan 5.1 da ba su
  yi rajista ba a bara.
  Sanarwa ta kara da cewa biyan kudin da kuma janye karar wani bangare ne na neman sulhu a wajen kotu.
  A watan Oktobar 2015 ne dai hukumar ta sanya wa MTN tarar $5.2 billion, amma daga bisani aka rage tarar zuwa Dala Biliyan 3.9 bayan MTN ta nemi rangwame.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here