Sojoji sun dakile hari a Dikwa

0
1847

Rabo Haladu Daga Kaduna
Rundunar sojin Nigeria ta ce a ci gaba da
kokarin da dakarun sojin keyi don
tarwatsa sansanonin \’yan Boko Haram a
garuruwan Kumshe da Talala da ke kan
iyakokin Najeriya, dakarun hadin gwiwar
kasashen Najeriya da Kamaru sun dakile
wani hari da mayakan suka yi kokarin
kaiwa a sansanin \’yan gudun hijra da ke
Dikwa.
Dakarun na musamman sun kuma samu
nasarar kashe mayakan Boko Haram da dama
tare da kwato makamai da kuma motoci daga
hannunsu.
A cikin wata sanarwa da kakakin sojojin kasa
na Najeriya, Kanal Sani Usman Kuka Sheka ya
sanyawa hannu, ta ce a yayin gwabzawar
tsakanin mayakan Boko Haram da Sojojin, an
kashe wani soja guda da kuma wani dan
kungiyar JTF.
Kazalika wasu sojoji uku da kuma \’yan gudun
hijra hudu sun samu raunuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here