Ba Za Mu Bari Kamfanin Da Sardauna Ya Kafa Ya Lalace Ba- El Rufa\’i

0
1128

IMRANA ABDULLAHI

\”GWAMNAN Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa\’i ya bayyana takaicinsa da ganin yadda aka bar katafaren ginin nan da ke tsakaiyar garin Kaduna, mallakar kamfanin buga jaridun NNN da GTK da aka fi sani da Nagwamatse House yana neman lalacewa ba tare da masu alhakin kula da kamfanin da ma\’aikatansa sun yi wani abin da za su ceto shi daga wannan mawuyacin hali ba.

Gwamnan ya ce \’\’Irin wannan al\’amari idan ba gwamnati ba babu wanda zai yasar da kadarar babban bene da ya shekara 40 da ginawa amma a bar shi cikin wani hali\”

Wadannan na daya daga cikin irin kalaman da Gwamnan Jahar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El Rufa i ya rika yi a lokacin da ya kai ziyarar gani da idanunsa tare da mukarrabansa kamfanin buga jaridun New Nigeria fa Gaskiya Ta Fi Kwabo a yau Juma\’a da misalin karfe 3:00 na rana bayan an sauko daga sallar juma a.

Gwamna Wanda ya isa harabar kamfanin tare da wata babbar tawagarsa ya isa kamfanin NNN ne wanda Marigayi Sardaunan Sakkwato ya kafa inda ya duba wani katafaren babban bene mai hawa 10.

 

 

\"IMG20160226155303\"

Inda ya ce, \’\’shin wai idan ba gwamnati ba wa zai yi irin wannan a gina abu bayan shekaru 40 da yinsa a bar shi a lalace duk da amfaninsa ta fuskar ci gaban jama a. \”Muna sa ran nan da wata daya mai zuwa gwamnonin arewa za su yi taro kuma muna sa ran a wajen wannan taron za mu tattauna abubuwa da dama, shi ya sa na zo domin gane wa idanuna irin halin da kamfanin yake ciki domin in yi bayani sosai.Amma mun sha alwashi tare da lasar takobin ganin cewa ba za mu bari abin da Sardauna ya kafa ba ya lalace haka nan, don haka za mu tabbatar komai ya yi daidai ta yadda jama a za su amfana\”.

Idan za a iya tunawa marigayi Sardaunan Sakkwato an kashe shi me a shekarar da ya bude kamfanin NNN kuma an ci gaba da aiwatar da aikin wallafa da buga jaridu har a kwanan baya ma aka yi bikin cikar kamfanin shekaru 50 da kafuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here