‘Yan Sanda Sun Kama ’Yan Fashi da Barayi 40 A Neja

0
1139

Daga Usman Nasidi

RUNDUNAR ’Yan sandan Jihar Neja ta kama kimanin mutum 40 a sassan jihar da ake zarginsu da yin fashi da makami.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Alhaji Abubakar Marafa ya bayyana haka a Minna inda ya ce rundunarsa ta lashi takobin ci gaba da dakile miyagu a jihar.

Kwamishinan ya ce zai dauki matakin da ya kamata domin kara wa jami’ansa gwiwa domin samar wa mutanen jihar damar gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali.

Alhaji Abubakar Marafa ya ce, daga lokacin da ya iso jihar a bara ya lashi takobin sa kafar wando daya da duk masu tayar da zaune- tsaye.

“Na yi imani kun fara ganin sakamakon alkawarin da na yi yayin da na kama aiki,” inji shi.

Kwamishinan wanda ya danganta karancin kayan aikin da ma’aikata da manyan matsalolin da suka kasance karfen kafa ga rundunar.

Ya yaba da hadin kai da kungiyoyi da daidaikun jama’a ke ba rundunar, inda ya nemi  jama’a su ci gaba da samar da muhimman bayanan da za su sa a dakile miyagun da ke barazana ga rayuwar jama’a.

Kwamishinan ya yaba wa Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello kan taimakon da yake ba su a matsayinsa na shugaban tsaro a jihar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here