Mahdi Shehu Ya Tallafa Wa Jami\’ar Jahar Kaduna Da motar Kashe Gobara

0
2103

A kokarinsa na ganin an tallafa wa daukacin al\’umma domin rayuwarsu ta ci gaba da inganta attajirin da ke zaune a cikin garin kaduna shugaban kamfanin DIALOGUE LTD Alhaji Mahdi Shehu,ya bayar da motar kashe gobara ga jami\’ar jahar kaduna.

An kuma yi wannan kwarya kwaryan taro ne na mika makullan motar a harabar jami\’ar da ke kan titin Tafawa balewa a cikin garin kaduna

Da yake mika makullan motar, Alhaji Mahdi Shehu ya bayyana cewa ya yi tunanin bayar da wannan mota ce sakamakon wata gobara da Jami’ar ta yi a kwanakin baya, inda sai da motar kamfaninsa ta taso daga nisan duniya don ta agaza wajen kashe gorarar, wanda inda suna da tasu, ba sai an jira wasu ba, “don haka ne na ga ya kamata a taimaka masu da tasu ta kansu,” in ji shi.

Alhaji Mahdi, wanda ya yi suna wajen bayar da irin wannan tallafi, ya ci gaba da cewa ya bayar da wannan tallafi ne domin taimaka wa Jami’ar wajen magance asarar rayuka da dukiyar Malamai, dalibai da sauran kadarorin Jami’ar.

Ya ci gaba da cewa, duk a tsawon wannan lokaci, bai kamata   a ce Jami’a kamar KASU ba ta da motar kashe gobara ba, wacce ya ce Jami’a ce mai dauke da al’umma da dukiya masu yawan gaske.

Don haka sai ya yi kira ga sauran masu hannu da shuni su ziyarci wannan jami’a domin duba irin gudumawar da za su bayar don inganta harkar Jami’ar, musamman abubuwan da za su ciyar da ita gaba, ta yadda za ta tsere wa tsara. Wanda ya ce duk mutumin da ya san wannan Jami’a a shekaru goma da suka gabata, ya ga yadda take a yanzu, zai tabbatar da cewa an yi amfani da ilimi, da kwarewa wajen ingantata.

Da yake amsa tambayar manema labarai game da ko yana yin wadannan  abubuwa ne don yana da burin siyasa a nan gaba kuwa, Alhaji Mahdi cewa ya yi shi ba ya siyasa, ba ya kuma sonta. Ya ce, “ba na son siyasa, ba na yinta, ba kuma zan yi ba.”

Da yake jawabi wajen a lokacin da yake karbar  makullan, Shugaban Jami’ar, Farfesa Barnabas Qurix ya bayyana matukar jin dadinsu da godiya game da wannan tallafi da attajirin ya kawo masu. Wanda ya ce shi ne da kashin kansa ya yi shawarar tallafa masu, ba su ne suka meni ya tallafa masu ba.

Shugaban ya kuma bayyana cewa ba wai mota kawai Alhaji Mahdi ya ba su ba, ya hada masu har da ma’aikatan kashe gobarar da za su yi aiki da ita. Wanda ya ce zai taimaka masu wajen magance duk wata  gobara da ka iya tashi a Jami’ar, duk da dai ba a fatan haka.

Daga nan sai Farfesa Qurix, ya tabbatar wa da Alhaji Mahdi cewa za su ba wannan mota kulawa ta musamman don ganin tana cikin koshin lafiya a kowane lokaci.

Da yake amsa tambayar manema labarai  game da yadda aka yi jami’ar ba ta da motar kashe gobara a duk wannan shekarru da ta yi, Farfesan cewa ya yi gwamnatin jihar ta yi oda a kawo masu, kuma tana nan a hanya, za ta iso nan ba da jimawa ba.

Wakilinmu ya shaida mana cewa Alhaji Mahdi Shehu, ya yi fice wajen bayar da taimako a bangarori da dama a karkashin wannan kamfani na DIALOGUE LTD, inda a ’yan kwanakin nan ma wannan kamfani ya kammala wani horar dadxalibai masu shirin zana jawabawar JAMB, wanda aka gabatar da ofishin kamfanin da ke Rigasa, Kaduna, wanda yara matasa kimanin 10, 000 suka amfana.

Bugu da kari Alhaji Mahdi Shehu,shi ne mutum daya tilo da Allah ya wadata shi da dimbin arziki amma dare da rana aikinsa shi ne samar da inganta al\’amuran lafiya,ilimi da sauran fannonin da jama\’a za su amfana musamman idan kaje asibitinsa da ke unguwar Dosa a yan majalisu duk wanda yaje zai ga kamar yaje kasar waje ne inda ake lissasu da cewa sun ci gaba to nan ma ya kawo wannan ci gaban a arewa.

Ga kuma makarantarsa da take a unguwar shanu a kan titin ali Akilu duk wanda ya shiga zai ce ba a Najeriya yake ba amma kuma a kaduna ya gina wannan makarantar ga wuraren sayar da magani mai kyau inda ake sayar da ingantattun magunguna duk wannan fa al\’amari ne na kishin jama\’a.

Ga kuma batun motar kashe gobara ta al\’umma duk ya yi ne domin a taimaki jama\’ar kasa baki daya,kaji inda ya sha bamban da masu samun dukiya ya su kai kasashen waje su boyeta wadanda ake yi wa kirari daga kwauri sai gwiwa,kun ga Mahdi Shehu ya cancanci jinjina a kodayaushe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here