Sanata Shehu Sani Ya Raba Littattafai Na Dala Dubu 30.

0
1406

IMRANA ABDULLAHI, Daga Kaduna.
SANATAN  da ke wakiltar Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawa ta kasa, Shehu Sani ya bayar da kyautar Littattafai na koyon harkokin kimiyya da fasaha da kimiyyar tattalin arziki da sauran fannoni na kimanin kudi Dala Dubu talatin domin amfanin daliban jami\’a musamman ga masu amfani da dakin karatu na gwamnatin tarayya da ke cikin garin Kaduna.

A lokacin da mai kula da dakin karatun ke tofa albarkacin bakinsa a dakin taro na dakin karatun na kasa, Muhammad Ndagi,ya bayyana matukar farin cikinsa da wannan kokari na Sanata Shehu Sani lamarin da ya bayyana a matsayin abin da zai taimaki al\’umma da ma al\’ummar da ke zuwa ko a nan gaba.

Shehu Sani ya ce abin da ya sa shi aiwatar da irin wannan aikin shi ne ganin cewa babu wani abu da ya fi bayar da ilimi ga yara matasa domin ta hakan ne kawai za su iya amsa sunansu na manyan gobe bayan samun ingantaccen ilimi.
\”Wani abu da ke daure wa jama\’a kai shi ne irin yadda majalisa ta gudanar da bincike ta kuma gano cewa da akwai \’yan Najeriya da suke karatu a kasashen waje da suka hada da Turai da kuma Nahiyar Asiya har miliyan daya kuma suna biyan kudin makaranta makudai da suka kai Dala Biliyan daya wanda ya isa a gina jami\’o\’i irin na Amurka akalla 15 amma ana bayar da kudin haka kawai ga wasu kasashe\”.

Shehu ya ci gaba da cewa da akwai wani al\’amari mai hargitsa tunanin mutum irin yadda wasu mutane daga wadansu kasashe ke zuwa Najeriya su kafa makarantu masu zaman kansu amma kuma sai su ce ba za su karbi kudin Najeriya ba sai Dala, ko Yuro da kuma  Fam na  na ingila kuma suna cikin Najeriya.

Sannan sai su ce ba za su koyar da karatun ba ma sai na kasarsu kuma suna cikin kasaitacciyar kasa Najeriya.

Sanata Sani ya kuma kudiri aniyar ganin ya kai irin wannan gudunmawa ga sauran makarantun da suke a karkashin mazabarsa domin ganin ilimi ya inganta.

Ya kuma ce kamar yadda kowa ya sani irin yadda ake ganin kafafen sada zumunci da muhawara na zamani sun kawo ci gaba haka nan kuma da akwai nakasu a fannin kin barin yara su yi karatun da ya dace inda ya ce idan mutun bai yi ilimi ba babu abin da zai rubuta a kan dandalin yanar Gizon sai shirme, don haka masu hannu da shuni da kuma iyaye sai su tashi tsaye domin samun ilimi mai inganci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here