An Gano Ma\’aikatan bogi 229 A Jahar Kaduna

0
1339

Rabo Haladu Daga Kaduna
GWamnatin Jihar Kaduna ta gano tare da korar ma\’aikatan bogi guda 229.
Wannan sanarawa ta fito ne daga ofishin baban akanta janar na jihar Kaduna Alhaji Waziri Umar Hassan, dauke da sanya hannunsa.
Acewarsa Gwamnatin jihar ta yi hakanne ba don cin mutuncin wani ko wata ba sai dai kawai kokarinta na tsaftace ma aikatun gwamnatin jihar tare da kawo inganci kyakkyawa ta yadda kowa zai gamsu da cewa ansamu canji.
Baban akanta janarjanar din ya CE idan aka duba takardar za a ga cewa a cikin alamomin da aka gano ma\’aikatan na bogi sun hadar Lamba tana zuwa daya data wani sai kuma suna shima sukancanja baki daya ko sukara ya ce musali Igb0625 Mohammed Amina kuma iri daya Mohammed Amina Igb1457,
Sai kuma sun yi kokarin jin ta bakin kungiyar kodago ta jihar kaduna inda suka nuna cewa baza su yardaba, sabo da yawancin wadanda akakora sunfi sama da shekaru 20 suna aiki bazai yiwu daga zuwan gwamnati kamar tanafishi dasu ba, tace ta kori maikata dari biyu da ashirin da tara,batare da zaunawa dasuba.
Acewar su zasu yi duk maiyiwa domin ganin hakan batatabbataba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here