Duk Mai Rike Da Sarautan Da Ya Ba Wani Fili Ya Taka Doka

0
1398

IMRANA ABDULLAHI Daga Kaduna
GWAMNATIN Jahar Kaduna ta fito fili ta fayyace cewa babu wani Hakimi,Dagaci ko Mai Unguwa da dokar kasa ta amince masa ya rika bayar da filaye balantana sayarwa jama\’a.

A duk cikar dokokin da ake da su a kan maganar filaye babu inda wata dokar jahar kaduna koma ta kasa baki daya ta yi maganar wani mai sarautar gargajiya ya sayar ko bayar da fili ga wani ko wasu.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Ibrahim Hussaini,Darakta Janar na hukumar kula da bayanan filaye ta Jahar Kaduna wato \”KADGIS\” ya bayyana hakan ne lokacin da ya amsa Goron gayyata a kan yazo cibiyar yan Jarida ta Jahar Kaduna domin yin bayanin yadda lamarin yake a doka bayan da al\’ummar unguwar huno 2 suka koka a game da maganar filayensu.

Ibrahim ya ci gaba da cewa a duk cikar dokokin filaye a fading tarayyar Najeriya har ma da duniya baki daya, kasa ta gwamnati ce kuma za ta iya Karba a lokacin da take son yin amfani da wuri sai dai da akwai tsarin biya diyya ga mai amfani da filin da ke cewa NASA ne amma wannan ma akwai tsarin da aka tanada.

\”Duk wani mai sarautar da ya sayarwa da wani ko wasu filaye to lallai yaje ya mayar masu da kudinsu musamman a bangaren inda gwamnati take kokarin yin ginin gidaje 2000 a wajen Dan Bushiya da ake kiransa da sunan Millenium city a gabas da garin kaduna\”.

Ibrahim Hussaini ya tabbatar wa manema labarai cewa a yanzu haka ana can ana aikin kididdiga da idan an kammala shi za\’a yi batun biyan diyya ga jama\’a, amma ba kamar yadda wasu ke cewa wai sun saya ko wani mai sarauta ya ba su ba wannan ba tsarin doka bane sam.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here