EFCC Ta Gurfanar Da Alex Badeh A Kotu.

0
1513

Rabo Haladu, Daga Kaduna.
HUKUMAR da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, ta gurfanar
da tsohon Babban hafsan sojin Najeriya, Air Marshal Alex Badeh, mai ritaya a babbar
kotun Abuja.
Hukumar ta zargi Mista Badeh da laifin satar kudi mallakin Rundunar sojin sama ta
Najeriyar kimanin Dala Miliyan 14, a lokacin da yake babban hafsan sojin kasar, domin sayen
filaye.
Rahotanni sun ce Mista Badeh ya gina katafaren gida na kasaita har ma da rukunin
shaguna.
Mista Badeh dai ya musanta wannan zargi. Air Marshal Badeh mai ritaya shi ne tsohon
babban hafsan sojin Najeriya karkashin mulkin shugaba Goodluck Jonathan.
Yana daga cikin wasu manyan jiga-jigan tsofaffin sojojin kasar da EFCC ke gudanar da bincike a kansu, bisa zarginsu da almundahana.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here