An Bude Manyan Hanoyin Da Suka Hade Maiduguri Da Sassan Kasar Nan

0
1187

Daga Usman Nasidi

A karshen makon jiya ne Babban Hafsan Sojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai, ya kaddamar da bikin bude manyan hanyoyin da suka hade birnin Maiduguri da wasu daga cikin kananan hukumomin jihar, bayan sun kasance a rufe kusan shekara uku.

Daya daga cikin hanyoyin ita ce wadda ta tashi daga Maiduguri zuwa Damboa mai nisan kilomita 85.

Sakataren kungiyar Direbobi ta kasa (NURTW) reshen Jihar Borno, Alhaji Amadu Musa ya bayyana bude hanyoyin da cewa ci gaba ne domin harkokin sufuri da cinikayya za su farfado a yankin da yake hanyar ta hade manyan birane.

Ya ce “Direbobi za mu bi wannan hanya da zarar an bude su, matukar fasinjoji za su bi za mu yi iya kokarinmu mu ga cewa mun biya wa jama’a bukatunsu. Sai dai kuma muna bukatar a inganta matakan tsaro wato a sanya shingayen binciken ababen hawa a kan hanyoyin ta haka ne kawai hanyar za ta samu ingantaccen tsaro a kowane lokaci.”

Da ya juya ga ’yan uwansa direbobi, Alhaji Musa ya hore su kan su kasance masu bin doka da oda tare da kiyaye lafiyar matafiya ta yadda za a ga alfanun bude hanyar, su kuma fasinjojin su bai wa Direbobi cikakken hadin kai da goyon baya domin kwalliya ta biya kudin sabulu.

Ciroma Goni Kashim, shugaban kungiyar matasan sa-kai ta Sibiliyan JTF da ke garin Damboa, ya nuna farin cikinsu ne dangane da bude hanyar kuma ya ce, “Za su yi iyakar kokarinsu wajen taimaka wa jami’an tsaro don samar da ingantaccen tsaro a hanyar, kuma za su yi kokarin kare rayuka da dukiyar jama’a.”

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here