An Hana Shigar Da Shanu Maiduguri.

0
949

Rabo Haladu, Daga Kaduna.

GWAMNATIN Jihar Borno ta hana shigar da shanu daga yankunan kananan hukumomin jihar.
Gwamnatin ta ce ta dauki matakin ne domin ta gano wasu bata-garin dillalai da suke hada baki da ‘yan Boko Haram wajen satar shanun a sayar wa jama’a.
Ana kuma zargin suna amfani da kudaden da suka samu daga sayar da shanun satar, wajen
gudanar da aikace-aikacen Boko Haram.
Gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima ya ce daga yanzu za a kara sojoji a kan fararen hula
wurin kula da gudanar da harkoki a kasuwar sayar da shanu da ke Maiduguri.
Har ila yau kuma Gwamnan ya hana sayar da kilishi. Kazalika, ya tsaurara matakai a gidajen yankan dabbobi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here