Kamfanin Tumatur Na Dangote Ya fara Aiki

  0
  1733

  Rabo Haladu Daga Kaduna
  Kamfanin sarrafa Tumatur na Dangote da ke Jihar Kano  ya fara aiki.
  Wadanda suka kafa masana\’antar dai sun ce kayan kamfanin zai yi gogayya da wadanda ke shiga Nigeria daga kasashen waje.
  Sama da dala miliyan 30 ne aka kashe wajen kafa masana\’antar, wacce manoma suka jima suna jiran zuwan ta domin  rage musu asarar da  suke tafkawa.
  Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da manoma kayan gwari ke kokawa da asarar miliyoyin nairorin da suke tafkawa, sakamakon rufe kasuwar Mile12 da aka yi a jihar Lagos bayan rikicin da aka yi tsakanin Hausawa da Yarbawa.
  Wasu daga cikin manoman sun ce su na da kwarin gwiwa ce wa za su samu sassauci akan halin da suke ciki, kuma sun gamsu da farashin da kamfanin ya ke biyan su akan kowanne kilo daya na tumari.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here