Yan majilasar Jihar Kano 34 sun Jefar Da Jar Hula

  0
  1488

  Rabo Haladu Daga Kaduna

  \’Yan majalisar jihar Kano kimanin 34 ne
  suka cire jajayen hulunansu, domin nuna
  goyon bayansu ga gwamna Abdullahi
  Ganduje kan sabanin da suka samu shi da
  tsohon gwamnan Sanata Rabi\’u Musa
  Kwankwaso.
  \’Yan majalisar sun yi alkawarin ba za su sake
  sanya jajayen hulunan ba, wadanda duk wani
  dan jam\’iyyar APC a jihar Kano ke sawa tun
  zamanin mulkin Kwankwaso a 2011 don nuna
  mubaya\’arsu gare shi.
  Kakakin majalisar Kabiru Alhassan Rurum ne ya
  jagoranci cire jar hular inda ya rage mambobin
  majalisar shida ne kawai ba su bi sahunsa ba
  wajen yin hakan.
  Honorabul Rurum ne ya jagoranci tawagar \’yan
  majalisar zuwa gidan gwamnati don ziyarar ban
  girma ga gwamna Ganduje, inda a can ne suka
  cire hulunan tare da neman gwamnan ma ya
  cire tasa jar hular.
  Sai dai a nasa bangaren, gwamna Ganduje ya yi
  kira ne ga \’yan majalisar da kada su rabu da
  jajayen hulunansu.
  Ya kuma shawarce su da su ci gaba da amfani
  da su a wata alama ta nuna girman jam\’iyyarsu
  a jihar Kano.
  A baya-bayan nan ne dai aka samu sabani
  tsakanin tsohon gwamna Rabi\’u Kwankwaso da gwamna Ganduje, inda al\’amarin ya jawo tayar da jijiyar wuya tsakanin magoya bayansu.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here