Gwamnatin Jahar Kaduna Da Ma\’aikata An Shiga Rudani

0
1554

IMRANA ABDULLAHI Daga Kaduna

A yau ranar Asabar 19 ga watan 3 2016 daukacin shugabannin kungiyar kwadagon tarayyar Najeriya karkashin jagorancin Kwamared Ayuba P Waba, suka sauka a dakin taro na sakatariyar kungiyar da ke kan titin Lafiya da Indifenda India suka tattauna da bayyanawa ma\’aikatan gwamnati kada Wanda ya sake ya cika takardar da gwamnatin ta bayar.

 

\"kwadago

Kwamared Ayuba Waba, ya shaidawa duniya cewa takardar da gwamnatin ta bayar a Jahar Kaduna cewa wait kowane ma\’aikaci ya bayyana mata cewa ko wace kungiya yake lallai lamarin ya saba wa dokar aikin gwamnati ta duniya ba Najeriya kadai ba.

Ya ci gaba da cewa kada fa gwamnatin Jahar Kaduna ta rika tsammanin cewa duk irin jin dadin da ma\’aikata ke yi suna samun sane ta jin dadi.

\”Duk lamarin yancin yayan kungiyar kwadago ana samun sane ta hanyar gwagwarmaya kuma don haka na yanzu ba zai zama daban ba kuma dole ne aba ma\’aikata yancin da tsarin yarjejeniyar aiki ya ba su\”.

Run a shekarar 1940 ma\’aikata suka samu yancin su kasance da kungiyar kwadagon da suke so domin ci gabansu haka take a rubuce haka make tafiya don haka ba canji domin son ran wani ko wash.

\”Ni shugaban kungiyar kwadago INA bayar da umarnin cewa kada wani ma\’aikaci ko ma\’aikaciya su sake su cika wannan takardar da gwamnati ta bayar a cika, ta yaya bayan an kammala tantance ma\’aikata kuma za\’a kawo wani fom a cewa ma\’aikata su cika?

Ya dace duk abin da za\’a yi ya zamanto da akwai wakilcin jama\’a musamman naa ma\’aikata, amma a tsari irin wannan said dai gwamnati kawai a wayi gari ana gaya wa jama\’a su cika takardar da babu wakilcin ma\’aikata wajen tsara ta hakan bai yi wa ma\’aikata dadi ba.

 

 

\"kwadago

\"kwadago
Da wakilinmu ya tuntubi shugabar ma\’aikata na Jahar Kaduna Kwamared Adamu Ango ko ma\’aikatan Jahar Kaduna su NASA me sai ya CE shi dai ya san da akwai ma\’aikata dubu 27 a matakin Jaha sai kuma dubu 36 a matakin malaman makaranta don zai iya cewa a kalla dubu 70 ko a samu sama da hakan

Amma tuni ya bayar da sanarwar kada Wanda ya cika takarda idan mutum ya cika ma kada ko ta sake ta mayar domin da akwai zaman taro a ranar Laraba mai zuwa da make gayyatar daukacin ma\’aikata ko wakilcinsu domin tattaunawa da kuma cimma matsayar abin da za ayi na gaba.

Indai za\’a iya tunawa kungiyar ma\’aikata sun shiga wani yanayin tantance su tun a kwanan baya inda lamarin ya rika haifarwa da ma\’aikatan rudu daban daban sai kuma ga wannan takardar da ake son sai kowane ma\’aikaci ya cika

Abin jira a gani shi irin yadda lamarin zai kasance a wannan yanayin rudanin da aka shiga tsakanin bangarorin biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here