Zamu Rufe Jahar Kaduna Baki Daya – Yan Kwadago

0
1490

IMRANA ABDULLAHI Daga Kaduna

 

GAMAYYAR kungiyoyin kwadago da ke tarayyar Najeriya sun bayyana kudirin su na ganin sun kwaci yancinsu ko ta halin yaya daga gwamnatin Jahar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmad El-rufa\’i, da suke zargi da kokarin tauyewa ma\’aikata yancin da dokar kasa da kuma tanaje tanajen kundin tsarin mulkin kasa ya ba su.

Wannan gargadi dai ya fito fili ne a lokacin da suka yi taron gangamin yayan kungiyar a Kaduna, inda suka ce sun ba gwamnatin El- rufa\’i, wa\’adin kwanaki Bakwai da ta canza tunanin da take yi a kan shisshigin da take kokarin yi wa dokokin kwadago na kasa da kuma na duniya baki daya.

 

 

\"Mata

Kamar yadda shugaban kungiyar kwadago na kasa kwamared Ayuba Waba, ya shaidawa taron dubban yayan kungiyar sama da su dubu 70 a harabar ofishin kungiyar da ke cikin garin Kaduna ya ce lallai su sani daga yau sun ba gwamnatin da Nasiru El- rufa\’i, yake yi wa shugabanci wa\’adin kwanaki 7 da ta canza tunanin da take na kokarin yi wa dokokin kwadago karan tsaye in kuma ba haka ba za su tabbatar da sun yi duk abin da doka ta tanadar domin kwato yancin ma\’aikatan jahar Kaduna.

Abin da ya bayyanar da cewa sun hada da \”a halin da ake ciki Lauyoyin kungiyar tuni sun rubuta wa gwamnatin kaduna takarda, sai kuma batun zuwa kotu sai kuma dauko yayan kungiyar akalla mutane 100 zuwa 150 daga ko wace Jiha domin su taru a kaduna daga ofishin kwadago zuwa gidan gwamnatin Jahar Kaduna domin tambayar gwamnan tambayoyin da suke son ya amsa masu.

 

 

\"Ma\'aikatan

Ya kwadagon da sauran kungiyoyi da dama sun tabbatar wa gwamnati cewa za su rufe Jahar Kaduna baki daya ta yadda komai zai daina aiki tun daga kan makarantu,ma\’aikatun gwamnati da masu zaman kansu,Bankuna,kasuwanni,motocin haya da daukacin gidajen mai da dai komai baki daya har sai an tabbatar wa da ma\’aikatan gwamnatin jahar yancinsu kamar yadda doka ta tanadar.

Wani abin mamaki ma a wajen wannan taro shi ne irin yadda mata ma\’aikata suka yi fitar dango domin halartar taron abin da ko su shugabannin kungiyar suka ce ba sabun ba domin ba\’a saba ganin hakan ba a can baya, koda yake shugabannin sun ce komai sai da mata kuma ko zabe ne sai da mata ake samun nasara kamar yadda gwamnatin jahar Kaduna ta bayyana cewa mata sun taka rawar ganin wajen fitowa domin zabar wannan gwamnatin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here