\’\’YAN SANDA NA NEMAN TAIMAKON UBANGIJI – Sifeto Janar

0
1208

DAGA USMAN NASIDI

A ranar lahadin da ta gabata ne lokacin wannannin yan sanda karo na 11 Sifeto Janar na yan sandan Najeriya ya bayyana cewa yan sandan kasar na neman taimakon Ubangiji domin yin aikin su yadda ya dace.

Sifeton Ya bayyana haka ne a Abuja a Cibiyar kirista ta kasa, a ranar Lahadi 27 ga watan Maris lokacin addu’o’i domin buda wasa karo na 11 wanda yan sanda ke gudanarwa.

Ya ce ” Karin neman imani da ubangiji yana da amfani ga dan sanda domin ubangiji ne ke sanya ikonnsa a cikin mu, duk da cewa aikin mu yana da wahala, domin mu kare mutanen kasa.
” Idan kai ma’aikacin banki ne, idan kayi kuskure asarar kudade za’ayi. Amma dan sanda idan yayi kuskure rai za’ayi asara. Muna bukatar Ubangiji a tare damu domin kada mu tura mutanen mu inda ran su zaya salwanta.

A wani labarin kuma, shugabar WARDC ta nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya duba yadda \’yan sanda suka sayi karnuka har na Naira Miliyan 600.

Misis Ketefe ta bayyana cewa hakan da \’yan sanda suka yi ya saba wa tsarin kasa, idan aka duba al\’amuran cikin gida Najeriya, domin saye-sayen ba su dace ba a lokacin tsanin tattalin arziki a kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here