0
1615

‘YAN SANDA SUN KAMA MATA ‘YAN FASHI A JIHAR RIBAS

DAGA USMAN NASIDI

‘YAN sandan Jihar Ribas sun kama wata kungiyar mata guda 3 wadanda suke aikin fashi da makami da kuma garkuwa da mutane.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an kama kungiyar ne a ranar 28 ga watan Maris a matsugunin su da ke Rumuolumeni da ke a cikin Jihar.

Rundunar Yan sanda ta bayyana sunayen su da; Queen Eze – shekara 27, Osorachi –
Shekara 24, da Queen godspower shekara 22.
Najeriya dai, musamman kudancin Najeriya na fama da matsalolin garkuwa da mutane inda makonni kadan da suka wuce aka saki kawun tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Wannan na zuwa ne bayan kwanaki kadan da batan Kanar a sojin Najeriya wanda a jiya ne
aka ga gawar shi a wani waje.

A wani labarin kuma, sojojin Najeriya sun kama wasu mutane dauke da akwatin gawa
ciki da makamai a ciki.
Sojojin sun kama hanya su ne a kan hanyar Legas zuwa Ondo inda suka saje kamar za su je gida ne su kai gawar dan uwan su wanda ya rasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here