Matatar Mai Ta Kaduna Za Ta Soma Aiki

0
988

Rabo Haladu Daga Kaduna
SASHEN man fetur na gwamnatin tarayya  ya ce, cikin mako biyu nan gaba matatar mai
ta Kaduna za ta soma aiki.
Wannan mataki na da nufin ganin an kawo karshen matsalar karancin mai da \’yan Nijeriya
ke fuskanta.
A wata ziyara da suka kai matatar mai ta Kaduna masu fada a ji a harkar mai sun ce, da
zarar an samu danyen mai daga Warri matatar Kaduna za ta soma aiki.
Wasu na danganta matsalar mai da ake fama da shi a Nijeriya ga matsalolin da suka
dabaibaye matatun mai na Kaduna da Fatakwal da Warri.
Tun daga watan Janairu ne dai matatar mai ta Kaduna ta daina aiki sanadiyyar rashin samun
danyen mai.
Ko da a cikin mako mai ƙarewa ministan mai Ibe Kachukwu ya sanar da wani tsari da zai
bai wa kwararru damar gudanar da matatun mai na Nijeryia.
Matsalar karancin mai kusan za a iya cewa, ta ki ci, ta ki cinyewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here