REDIYON BIAFRA YA DAWO AIKI-KUNGIYAR IPOB

0
1018

DAGA USMAN NASIDI

REDIYON Biafra ya dawo aiki bayan da gwamnatin tarayya ta tsaida kama tashar a jihohin Najeriya.
Jami’i mai hulda da jama’a na Rediyon ta Biafra, Emma Powerful, ya bayyana cewa ” Yanzu muna aiki ne ta hanyar karamin zango wanda duka jihohin kudu maso Gabas za su iya kamawa tare da Jihohin Legas, Delta, Ribas, Kuros Ribas, Landan, Akwa Ibom da Bayelsa.
Ya kuma bayyana cewa a yanzu za’a iya kama tashar Rediyon ta hanyar waya da kuma application na waya.
Ya ce ” A yanzu mun dawo kan iska bayan da gwamnatin Najeriya ta kashe Miliyoyin kudaden jama’a domin ta toshe tashar Rediyon tamu.
Duka ‘yan Biafra da abokan Biafra za su iya samun mu yanzu a 11600kHz da karfe 8 na
yamma a Ingila, ko kuma karfe 9 na yamma a kasar Biafra. Ba za su iya tare mu ba saboda
Ubangiji Chukwu Okike Abiama yana tare da mu.
Idan za a iya tunawa, kwanakin baya kungiyar ta zargi gwamnatin tarayya, hukumar DSS ta hada kai don a kashe shugaban Rediyon Biafra, kuma shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.
Sun bayyana cewa za’a gudanar da kisan ne akan hanyar zuwa kotu sai a ce ya yi kokarin rugawa ne sai aka harbe shi da Bindiga.
Kungiyar kuma ta yi barazanar zanga-zanga a duka biranenn Najeriya domin kira ga Najeriya ta saki Nnamdi Kanu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here