An Yi Dambe A Majalisar Jihar Nassarawa

  0
  1160

  Rabo Haladu Daga Kaduna
  \’YAN majalisar jihar Nassarawa  sun ba hammata iska a yayin wani zaman
  majalisar a jiya, Litinin.
  Rahotanni na cewa \’yan majalisar sun zage damtse a inda suka kai wa juna duka har da
  jifa da tebur a yayin rikicin.
  \’Yan sanda sun shiga tsakani a yayin da mai kula da sandar majalisar ya samu nasarar tsira
  da ita ba tare da wani lahani ba.
  Kafofin yada labarai da suka rawaito lamarin sun ce nadin da Gwamnan jihar Tanko Al
  Makura ya yi na Kantomomin kananan hukumomin jihar ne makasudin wannan fitina.
  Wannan  rikici dai ba sabo ba ne a jam’iyyar ta APC inda mabiyan jam’iyyar suke kokawa da

  cewa wanda  ya sha wahalar jam’iyyar ba shi ke morarta ba, haka abin yake a sauran jihohin kasar nan.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here