DAN SHEKARA 12 YA TSALLAKE RIJIYA DA BAYA DAGA HANNUN MATSAFA

0
1231

DAGA USMAN NASIDI

A yammacin Lahadin da ta gabata ne Allah Ya kubutar da wani yaro mai suna Umar Usman Kwabren Dorowa mai kimanin shekara 12 daga hannun wasu mutane da ake zargin matsafa ne
masu amfani da sassan jikin mutane.
Umar Usman Kwabren Dorowa da ke zaune a Sabuwar Unguwa a birnin Katsina ya bayyana cewa “Zan je makarantarmu ta Islamiyya a nan unguwarmu bayan Sallar La’asar, na yi kusan isa daidai wani lungu sai wata mota kirar Golf 3 ta shigo hanyar. Suna zuwa inda nake, na tsaya don su wuce, kawai wadansu mutane suka fito suka kama ni da karfi suka sanya wani tsumma a cikin bakina don kada in yi kuka, suka sanya ni cikin motar suka danne ni a bisa kujera, suka ce in na yi kuka ko wani abu za su kashe ni.
Ya ce Ban san inda aka nufa ba har sai da muka je wani fili, sai suka ce, “mu jefar da tsinanne a nan. ” Sai suka bude motar suka jefo ni waje bayan sun kwance mini tsumman daga bakin.”

Yaron ya ce yana cikin kuka sai wani dan sanda ya zo zai wuce, da ya gan shi ya tambaye shi abin da yake yi wa kuka. Da ya gaya masa sai ya ce, “Na san inda nake? Na ce, a’a. Sai ya ce nan
garin Malumfashi ne, kusa da kotu ne,” inji yaron.

Umar ya ce, an jefar da shi ne a wurin, bayan Sallar Magariba, kuma a cewarsa, tun da suka taho bai ji sun tsaya a wani wuri ba. “Dukkansu da Hausa suke magana sai dai ba na jin abin da
suke cewa. Kuma suna sanye da bakaken kaya ne.  Kuma lokacin da suka sanya ni a cikin motar na ga wata yarinya kwance a wurin ajiye kaya na motar tana kuka amma ba ta magana. Na kuma
ga wuka ajiye kusa da ita da bindigogi biyu babba da karama,” inji shi. Umar ya ce, ba su yi masa komai ba har zuwa lokacin da suka jefo shi kasa.
Dan sandan da ya tsinci yaron, (wanda aka sakaya sunansa) ya kai shi ofishinsu da ke Malumfashi inda su kuma ba su yi kasa a gwiwa ba suka tuntubi Katsina, kuma bayan tabbatar da
inda yaro yake a cikin Katsina, sai suka hado shi da wani jami’insu ya kawo shi har gidan mahaifinsa da ke Kwabren Dorowa a ranar Litinin da ta gabata.
Mahaifin Umar, mai suna Malam Usman ya shaida cewa ya shiga cikin tashin hankali lokacin da suka fahimci Umar bai dawo gida ba. “Yarana kullum karfe 8:00 na dare suke kwantawa barci. To ganin an tayar da yara daga Islamiyya, muka ga har an yi Magariba Umar bai dawo gida ba, kuma abokan makarantarsa sun ce ba su gan shi ba, ya sa muka fara bincike a kai saboda bai taba yin haka ba.
Duk wata kafa ta sanarwa mun je, mun je asibitoci amma shiru. Saboda haka muka ci gaba da rokon Allah kuma Ya karbi rokonmu,”inji Malam Usman. Sai ya yi godiya ga ’yan sanda musamman na Malumfashi a kan wannan kokari da suka yi.
Hakazalika, a makon shekaranjiya sai da aka tsinci gawar wata yarinya mai kananan shekaru a Unguwar Sabon Gida wadda aka cusa wa tsumma a bakinta.
Wasu Ganau sun shaida cewa, bayan alamun fyade ga yarinyar an kuma kwakule dukan idanuwanta, a daidai inda aka taba tsintar gawar wani yaro da aka yi zargin bayan an kashe shi ne aka zo aka rataye gawarsa da igiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here