Majalisar Tsaron Jahar Kaduna Ta Hana Sayar Da Mai A Cikin Jarkoki

0
1324

Imrana Abdullahi Daga Kaduna

MAJALISAR kula da harkokin tsaro ta Jahar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmad El-Rufa\’i, ta fitar da wata sanarwa bayan kammala zamanta a yau Talata 5 ga watan Afrilu 2016 a gidan gwamnatin jahar da take cewa, an hana sayar da ma\’adinan man fetur a jarkoki a fadin jihar baki daya.

Majalisar ta ce daukar wannan mataki ya zama wajibi ganin irin yadda sayar da man fetur a cikin jarkoki yake da matukar hadarin gaske don haka ya zama wajibi a irin wannan lokaci ya kyautu a tabbatar da dokar Jihar Kaduna ta shekarar 1992 da ta yi cikakken tanajin sayar da Man Fetur a cikin Jarkoki da Galan-Galan abin da aka fi sani da suna Bumburutu.

Don haka daga yau a duk fadin kananan hukumomi 23 na Jaahr Kaduna an hana sayar da mai a cikin Jarkoki ko a Galan-Galan da ake cewa Bumburutu, kuma dole ne a bi wannan dokar tun da dama can akwaita shekaru da dama.

Daga cikin wadanda suka halarci taron sun hadar da daukacin majalisar sarakunan Jihar da kuma masu mukaman Cif-Cif sai daukacin jami\’an tsaron sojan kasa,Sama da na Ruwa, \’Yan Sanda,da suka hada da na ciki,jami\’an kulawa da hadurra ta kasa da suke aiki a Jihar Kaduna da sauran dukkan daukacin hukumomin tsaro domin tabbatar da nasarar gudanar da wannan doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here