Yan kasuwa ke haddasa tsadar shinkafa a Nijeriya

  0
  1454

  Hukumar hana fasa kwuri ta Najeriya wato
  kwastam ta zargi \’yan kasuwa da  haddasa tsadar shinkafar da
  ake fama da ita a yanzu haka a duk fadin kasar nan.

  Hukumar  kwastam ta ce \’yan kasuwar sun yi
  amfani da haramta shigar da shinkafar da aka
  yi ta iyakokin kasar, inda suke cewa an
  haramta shigo da shinkafar ne baki daya.

  Su dai \’yan kasuwar  na ɗaura alhakin
  tashin farashin da shinkafa ta yi kan matakin
  da hukumar ta hana fasa kwauri ta ɗauka na
  hana shigar da shinkafar ta kan iyakokin  kasar.

  A farkon wannan shekarar ne hamshakin mai
  Kudin nan na Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya
  Kaddamar da shirinsa na bunkasa harkar noma
  a jihar Jigawa da ke.
  Shirin dai wani bangare ne na yarjejeniyar da
  aka kulla tsakanin gwamnatin jihar Jigawa da
  kuma kamfanin na Dangote.

  An ware kadada 20,000 a jihar Jigawa, da za a
  yi amfani da su wajen gagarumin aikin noman
  shinkafar zamani, inda za a samar da shinkafa
  mai yawa don bunkasa sana, ar noma kasar.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here