\’Yan Shi\’a 347 Aka Yi Wa Jana\’iza A Kaduna

0
1566

Rabo Haladu Daga Kaduna

GWAMNATIN Jihar Kaduna ta bada ba\’asi a gaban kwamitin bincike kan
rikicin \’yan shi\’a da sojoji a ranar Litinin.
Gwamnati ta ce mutane 347 ne aka yi wa jana\’izar bai – ɗaya, sai dai kuma \’yan shi\’ar
sun bada ta su sanarwar, inda suka musanta adadin da cewa ya fi haka.
Sakataren gwamnatin Jihar Kaduna, Balarabe Lawal ne ya bayyana haka a wajen wani zaman bayar
da ba\’asi a gaban kwamitin binciken da aka kafa .
A karo na farko da gwamnati ke fayyace lamarin, sanarwar ta ce an binne gawarwakin
\’yan shi\’an ne a asirce.
A bayanin sakataren, wanda shi ne jagoran mutune shida da suka tabbatar da lamarin, ya
ce an binne gawarwaki 191 da aka dauko daga sansanin soja da ke Zariya, a Unguwar Mando
da ke Kaduna.
Ya kara da cewa akwai karin gawarwaki 156 da aka dauko daga asibitin Ahmadu Bello da ke
Zariya, wadanda su ma aka kai a Mandon.
Jami\’in gwamnatin ya ce gawarwakin na matasa ne \’yan kungiyar \’yan uwa musulmi, wato
Islamic Movement(IMN), wadanda ya ce an zarga da neman afka wa tawagar babban hafsan
sojojin kasar, Laftanar-Janar Tukur Buratai, a ranar 12 ga wata Disambar shekarar 2015.
Malam Lawal Balarabe dai bai bayyana ko iyalan mamatan sun samu damar ganinsu kafin
a kai ga binne su ba koko a\’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here