Siyasar Ubangida Na Kawo Rashin Ci Gaban Najeriya

  0
  1080

  Jabiru A Hassan, Daga Kano.

  AN bayyana cewa siyasar uban gida ita ce ta  jawo  rashin ci gaba a kasarnan tun lokacin da aka koma kan tsarin mulkin dimokuradiyyar wannan karni.

  Wannan tsokaci ya fito ne daga Alhaji  Abdu Dan Garba a zantawar sa da manema labarai a kano, inda ya tabbatar da cewa muddin za\’a ci gaba da yin siyasar uban gida babu wani ci gaba da za\’a samu  a kasarnan  har sai an koma bisa cancanta da dacewa a lokutan zabe.

  Ya ce abin takaici shine yadda iyayen gidan masu rike da madafun iko suke bada umarni  ga yaransu dangane da duk wani abu da suke da bukata tun da dama hakan ce ta sanya suke tsayar dasu takara  domin biyan bukatun nasu koda kuwa ba zasu zamo masu amfani ga  al\’uma ba.

  Daga karshe, Alhaji Abdu Dan Garba ya sanar da cewa da yardar Allah,  za\’a  kawar da siyasar uban gida a kasarnan, sannan shugaba Buhari zai canza fasalin siyasar kasarnan ta yadda  samun madafun iko zai  zamo sai wanda ya cancanta.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here