Sanata Barau Jibrin Ya Yi Watsi Da Mazabarsa – Tallo

  0
  1473

  Jabiru A Hassan, Daga Kano.

  Jagoran kungiyar matasan  mazabar kano  ta  arewa   Alhaji Mustapha Umar Tallo gwarzo ya nuna rashin jin dadin sa bisa yadda sanatan  mazabar watau sanata Barau Jibrin  ya yi watsi da matasan da suka jajirce wajen  tabbatar da ganin  ya  sami nasara  a zaben da akayi nana shekarar 2015.

  Tallo, Ya yi wannan korafi ne a zantawar su da wakilin mu, inda ya sanar da cewa matasan kano ta arewa sun taka muhimmiyar rawa wajen ganin ya zamo sanatan wannan mazaba, amma sai gashi ya yi watsi dasu  wanda hakan  ya nuna  cewa baya neman gudummuwarsu idan wani zaben ya sake zuwa.

  Alhaji Mustapha  Tallo ya kuma bayyana cewa  ana yin siyasa ne domin kawo ci gaba ga al\’uma, don haka ne ma suka jajirce domin ganin sanata Barau Jibrin ya lashe zabe saboda yarda da suka yi cewa zai  tabbatar da ganin  wannan mazaba ta kano ta arewa ta bunkasa kamar yadda sauran mazabu suke.

  Sai dai ya yi kira ga matasan kano ta arewa da su kara hakuri  su kuma baiwa sanatan karin lokaci ko Allah zai sa ya waiwayi talakawan

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here