\’Yan Bindiga Sun Sace Ma\’aikacin NNPC A Kaduna

0
1113

IMRANA ABDULLAHI Daga Kaduna

A wani al\’amarin da ke kama da almara ko kuma bakar sana\’ar da ke nema zama ruwan dare a Jahar Kaduna shi ne irin yadda wadansu da ba\’a san ko su waye ba suka sace ma\’aikacin NNPC mai suna Yusuf Abdulkadir da yake aiki a Hedikwatar kamfanin da ke Abuja.

Shi dai wannan lamari ya faru ne a unguwar Rigachikun da ke cikin garin Kaduna karamar hukumar Igabi da misalin karfe 10 na daren ranar Asabar da ta gabata.

Majiyarmu ta shaida mana cewa shi dai wannan ma\’aikaci na kamfanin tace mai wato  NNPC da yake aiki a Abuja yakan dawo gida ne a duk sati.

Wannan karon ma hakan ta faru Yusuf Abdulkadir, ya dawo gida Rigachikun da misalin karfe 10 na dare sai kawai masu satar mutanen suka nuna masa bindiga suka yi awon gaba da shi a ranar Asabar da ta gabata kuma kawo lokacin rubuta wannan labarain babu wanda ya san inda yake.

Wata majiya daga bangaren iyalan wanda aka sace din ta shaida mana cewa maharan sun yi ta binsa a baya har suka samun nasarar kama shi da kuma tafiya da shi wurin da a yanzu ba\’a san inda yake ba.

\”Sun yi ta binsa ne tun daga inda yake yana dawowa gida sun kuma tsare shi da bindiga suka tilasta masa fita daga motarsa suka kuma yi awon gaba da shi\”. inji majiyarmu.

 

Kamar yadda wani dan uwansa ya shaida wa majiyar ta mu cewa tuni sun rigaya sun kai wa yan sanda rahoton faruwar lamarin.

Sai dai mai magana da yawun rundunar yan sandan Jaihar Kaduna Zubairu Abubakar, ya shaida mana cewa ko da yake ba shi da masaniyar faruwar hakan amma dai zai tuntubi jami\’in DPO da ke kula da wannan yanki domin jin abin da ya faru kuma zai shaidawa wakilinmu abin da ake ciki nan gaba.

Amma dai abokin wanda aka sacen da suke aiki tare ya tabbatar da cewa lallai babu shakka an sace Yusuf Abdulkadir sai dai ya bukaci a sakaya sunansa a matsayinsa na mai aiki da gwamnati da ba shi da damar yin magana da manema labarai koda yake shima ya tabbatar wa majiyarmu cewa an kai wa Yan Sanda rahoto lokacin da lamarin ya faru.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here