0
1158

\’YAN SANDA SUN KASHE WANI MATASHI A JIHAR KADUNA

Daga Usman Nasidi

\’YAN sanda a Jihar Kaduna sun bindige wani matashi dan bunburutu har lahira a jihar Kaduna a daren ranar Alhamis ta makon jiya.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna da suka kaddamar da wani samame a wani gidan mai da ke Kaduna, inda ake zargin matasa ‘yan bumburutu ke cin kasuwar dare, inda suka tarwatsa gungun matasan tare da harbe daya daga cikinsu, wanda ake kyautata zaton shine jagoransu.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewar, lokacin da ‘yan sandan suka dira sansanin ‘yan bumburutun, sun yi ta harbi irin na kan mai uwa da wabi, inda matasan suka fasa da gudu, amma shi jagoran nasu mai suna Dan Aguro ya tsaya domin tattara jarkokin mansa, dalilin haka ‘yan sandan suka bindige shi.

Wakilinmu daya halarci gidan iyayen matashin da aka kashe dake Unguwar Shanu Kaduna,  ya tarar da cewar tuni an riga an yi jana’izar sa, yayin da jama’a ke amsar gaisuwar ta’aziyya.

Dukkanin kokarin da wakilinmu ya yi domin jin
bangaren rundunar ‘yan sandan jihar ya ci tura, sakamakon rashin daukar waya da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Zubairu Abubakar yake yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here