Sojoji Sun Fatattaki \’Yan Boko-Haram Daga Kareto

0
1043

Rabo Haladu Daga Kaduna

RUNDUNAR sojojin Najeriya ta ce dakarunta sun dakile harin da \’yan kungiyar Boko Haram suka kai musu a a kauyen Kareto da
ke jihar Borno.
Kakakin rundunar sojojin Kanal Sani Kukasheka Usman, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya aike wa
manema labarai, ya kara da cewa dakarunsu sun kashe \’yan kungiyar Boko Haram da dama.
A cewar sa, sojoji 22 ne suka samu rauni, kuma an kai su asibitin sojoji na Maiduguri domin yi
musu magani.
Tun da fari dai, rundunar sojin Najeriya ta ce \’yan kungiyar Boko Haram sun kai hari kan
dakarunta na Bataliya ta 113 da ke Kareto a arewacin jihar Borno.
Rahotanni daga jihar Bornon sun ce mayakan kungiyar Boko haram sun kai wa sojojin
Najeriya harin kwanton-bauna a garin na Kareto da ke kusa da kan iyakar Najeriya da
Nijar.
Kanar Sani Kukasheka Usman ya ce dakarun sun fafata da mayakan Boko Haram tun daga
sanyin safiyar ranar Litinin.
Wata majiya a rundunar sojin  ta ce wasu sojoji sun rasa rayukansu, yayin da
kuma wasu suka bata sakamakon harin.
Sai dai wani mazaunin yankin ya shaidawa manema labarai mcewar sojojin Najeriya sun kashe mayakan
kungiyar Boko Haram da dama kuma garin Kareto na karkashin ikon sojojin Najeriya a yanzu haka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here