An Nemi \’Yan Nijeriya Su Kara Juriya Domin Samun Ribar Dimokuradiyya

  0
  1132

  Jabiru A Hassan,  Daga Kano.

  AN bukaci \’yan Nijeriya da su kara  yin hakuri  bisa halin da kasa take ciki  kafin gwamnati mai ci ta shawo kan dukkanin matsalolin da suka dabaibaye kasa.

  Wannan bayani ya fito ne daga wani tsohon  dan siyasa, Alhaji Abdullahi Ahmed Kwa a tattaunawarsu da wakilinmu, inda ya sanar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yana da kyawawan manufofi ga al\’ummar kasar nan  a yankunan karkara da kuma birane.

  Sannan ya ce  idan aka sami canjin gwamnati a kasa, sai an dan dauki lokaci kafin a kammala yin tsare-tsare na tafiyar da gwamnati, don haka yana da kyau al\’ummar kasar nan su kara nuna juriya da hakuri kafin  nan gaba kadan a fara jin dadin canjin da aka samu.

  Alhaji Abdullahi Bature Kwa ya kuma nuna matukar jin dadin sa bisa yadda Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullhi Umar Ganduje yake tafiyar da gwamnatinsa tare da yin shiri mai kyau na bunkasa jihar, inda ya yi fatan alheri ga manufofin gwamnatinsa.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here