TSOHON GWAMNA ISA YUGUDA YA FICE DAGA JAM\’IYYAR PDP

  0
  1132

  Daga USMAN NASIDI

  TSOHON Gwamnan Jihar Bauchi, Isah Yuguda ya fice daga jam’iyyar PDP inda ya bayyana ficewar tasa a wayar salula da yake zantawa da manema labarai.

  Yuguda ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ba ta da manufa a yanzu, kuma ba za ta kawo wa Najeriya wani ci gaba ba.
  A inda yan jarida suke tambayar shi, Yuguda ya ki ya bayyana masu inda alkibilar siyasar shi za ta sanya gaba.

  Ya ce ” Na rigaya na gaya wa magoya baya na cewa ba zan tursasa su barin PDP ba, amma duk wanda ke so ya fita tare da ni ina yi mashi maraba.

  ” Jam’iyyar PDP ba za ta iya kawo wa Najeriya wani ci gaba ba a yanzu. Jam’iyyar ba ta da manufa a yanzu.

  Yuguda kuma ya yi kira ga alumma da su yi wa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’a domin ta ci nasara.
  ” Alkur\’ani ya umurce mu da mu ringa yi wa shugabanninmu addu’a. Ya kamata mu ringa yi wa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’a.
  Bayan da ya fadi wannan babu jimawa sai wasu daga cikin magoya bayan shi suka tafi Ofishin \’yan jarida reshen Jihar Bauchi inda suka yaga katinsu na jam’iyyar PDP a baynar jama’a.

  Yuguda ya yi kaurin suna sosai wajen canza jam’iyya a lokacin da ya ga dama, ya kasa samun takarar jam’iyyar PDP a shekarar 2007 inda ya canza zuwa ANPP inda ya ci Gwamnan Jihar. Jim kadan bayan haka ya koma jam’iyyar ta PDP din.

  Tsohon Gwamna ya yi Minista a lokacin tshon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here