MUTANE 6 SUN MUTU A GOBARAR WANI GIDAN MAN NNPC KADUNA

0
1137

 

DAGA USMAN NASIDI

SAKAMAKON wata gobara da ta tashi a wani gidan Mai na NNPC da ke a Kaduna, mutane 6 sun rasa rayukansu inda motoci1 5 suka kone ta yadda ba za ka iya shaida su ba.
Bincike ya nuna cewa gobarar ta fara ne da misalin karfe 5:09 na yamma inda ta yi ta ci har bayan awanni 3 da farawar ta.
Mataimakin shugaban gidan Man, Alhaji Jibril Musa, ya bayyana cewa a ranar Asabar da ta gabata ne a lokacin da wata mota ke saukar da mai sai ta kama da wuta inda ta kone kurmus.
Ya ce “Ba’a sanya ma man sosai ba. Bayan da Man ya zuba a kasa, wani mai mota ya gama shan man nashi inda yana kunna motarshi sai gobarar ta fara.
” Motoci 15 ne suka kone inda gobarar ta shafi gidan Mai na kusa da mu. \’Yan kwana- kwana sun zo inda suka fara kokarin kashe wutar.
Wata majiya da ta bada shaida, ta bayyana cewa, gidan man na kusa na Shammaco ne ya kama da wuta.
Ya ce “gobarar ta aiku kuma mu babu abunda za mu iya yi. Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukan su, Allah ya ba wadanda suka ji raunuka lafiya.
Inda aka tuntubi shugaban hukumar \’Yan Kwana-kwana ta Jihar Ka duna, Paul Abio, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya bayyana cewa ma’aikatan hukumar sun yi kokarinsu na ganin sun kashe wutar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here