Ya Yi Kira Ga \’Yan Adawar Gwamnatin APC Da Yin Adawa Mai Ma\’ana

  0
  1110

  Jabiru A Hassan, Daga Kano.

  AN bukaci \’yan siyasar kasar nan da su kasance masu yin adawa mai ma\’ana wadda  za ta taimaka wa masu rike da madafun iko wajen tafiyar da mulki ingantacce.

  Wannan kira ya fito ne daga Malam  Sani  Muhammad a tattaunawarsu da wakilinmu  a Kano, inda ya sanar da cewa ana yin adawa ne domin a zaburar da masu mulki ta yadda za su kara himma wajen yi wa al\’umma aiyukan da suke bukata, sabanin yadda ake yin adawa a wannan zamani  domin cin zarafin masu  mulki.

  Malam Sani Muhammad ya nuna cewa yana da kyau \’yan siyasar wannan lokaci su tsaya su duba abubuwan da suka kamata su yi wa al\’ummomin su, maimakon yin amfani da kujerunsu wajen azurta kansu  wanda a cewarsa hakan ba daidai ba ne, inda a karshe ya yi fatar cewa Nijeriya za ta bunkasa  kamar sauran kasashen duniya da suka bunkasa a yau.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here