An Sace Tsohuwar Ministar Ilimi

0
1287
\"Iyabo
IMRANA Abdullahi daga Kaduna
Rohotannin da muke samu a halin yanzu na cewa wadansu yan bindiga masu satar mutane sun sace tsohuwar ministar Ilimi a tarayyar najeriya mai suna iyabo ANISULOWO
ita dai wannan tsohuwar minista misis Anisulowo an sace ta ne da misalin karfe shida na Yammar ranar Laraba a Ilaro cikin karamar hukumar Yewa ta Kudu a Jihar Ogun,kamar yadda jami\’an yan sanda suka bayyana.
Muyiwa Adejobi shi ne kakakin rundunar Yan Sanda a Jihar Ogun ya tabbatar da faruwar lamarin da misali karfe 10 na daren ranar Laraba.
Inda ya tabbatar da cewa kwamishinan Yan Sandan Jihar ya Samar da karfafan rukunin ma\’aikata daban daban har kala boyar domin gudanar da aikin ceton minister.
Ita dai wannan mata ta zama minista ne a gwamnatin marigayi Sani Abacha tata kuma taba zama Year majalisar Dattawa mai wakiltar mazabar Ogun ta Gamma,ta kuma yi takarar gwamnan Jihar Ogun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here