DAKARUN SOJIN NAJERIYA SUN KAMA WANI KANAR DIN SOJA NA BOGI

0
1684

Daga Usman Nasidi 

A ranar Juma’ar data gabata ne rundunar sojojin Najeriya suka gurfanar da wani mai suna Prince Joshua Onyemauche wanda ake zargin sa da ikirarin  cewa shi Kanar ne na soja.
Mai magana da yawun sojojin kasa Kanar Sani Kukasheka Usman, a yayin da ake gabatar da wanda ake zargin ga manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Abuja, ya bayyana cewa an kama mutumin da bindigogi ciki har da kirar fistol.
Kakakin ya kara da cewa an kama Onyemauche ne tare da wasu sojoji ciki har da wani mai suna Sajan Jacob Phillip da misalin karfe 12 na dare a ranar 17 ga wannan wata, a kusa da tashar mota ta Wazobia da ke garin Gwagwalada a Abuja.
Ya ce mutumin yana tuka wata mota kirar  Toyota Tacoma ne a lokacin da sojojin  suka kama shi, bayan ya kubuce a karon  farko a shingen bincike a garin Abaji bayan  ya bayyana kansa a matsayin Kanar din soja.
Usman ya ce bayan an kama su ne sai aka garzaya da su barikin sojoji da ke Gwagwalada inda a yayin bincike aka gano bindiga kirar AK 47 mai lamba 3290 da kuma magazin guda hudu, wanda biyu daga cikin su ke dauke da harsashai.  An kuma gano kudi kimanin Naira Milyan daya da dubu sha daya da dari uku.
Kukasheka ya kara da cewa bincike ya nuna cewa Onyemauche yana amfani da sojoji biyun ne a duk lokacin da zai je jiharsa ta Imo daga Legas ba tare da izinin rundunar tsaro ba.
Ya kuma kara da cewa sojojin da suke raka shi din,za a mika su kotun sojoji domin yanke masu hukuncin da ya kamata.
Kanar Usman ya bayyana cewa za a mika Onyemauche ga ‘yan sanda domin ci gaba da bincikensa. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here