Ta Nuna Gamsuwarta Da Yadda EFCC Take Ayyukanta

0
1116

Jabiru A Hassan, Daga Kano.

KUNGIYAR  wayar da kan al\’umma kan illolin cin hanci da rashawa ta kasa reshen Jihar Kano ta nuna gamsuwar ta bisa yadda hukumar yaki da cin  hanci ta kasa wato EFCC take gudanar da ayyukan ta na tsaftace al\’amura a kasar nan.
Shugabaan kungiyar Alhaji  Garba Dan Malam shi ne ya bayyana haka ga wakilinmu jim kadan bayan kammala taron wayar da kai kan ayyukan hukumomi masu yaki da cin hanci wanda kungiyar ta shirya  ranar Talatar da ta gabata.
Ya ce ko shakka babu, Nijeriya ta tsinci kanta cikin wani mawuyacin hali na cin hanci da rashawa, amma da yardar Allah gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari za ta cimma nasarar farfado da martabar kasar nan a idon duniya ta yadda dan Nijeriya zai yi alfahari da kasarsa.
Malam Garba Dan Malam ya nunar da cewa wadanda suka yi satar kudaden al\’umma sun bada kunya domin kuwa a da ana yi masu kallon daraja da mutunci a kasa, amma sai ga shi sun zamo abin takaici saboda sace dukiyar kasa da suka yi.
Yayi kira ga shugaba Buhari da ya gaggauta  bayyana dukkan wadanda gwamnatinsa take tuhuma da yin halin bera ga dukiyar kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here