Sabon rikici ya ɓarke a PDP kan shugabanci

  0
  8228

  Rabo Haladu Daga Kaduna

  WANI sabon rikici ya sake ɓarkewa a babbar jam\’iyyar adawa ta  PDP, sakamakon
  kebe kujerar shugabanta na kasa ga shiyar arewa-maso-gabas, yankin da shugabanta
  na riko ya fito.
  Jiga-jigan jam\’iyyar daga shiyyar kudu-maso- yamma sun yi barazanar ficewa daga jam\’iyyar
  idan ba a bayar da kujerar shugabancin jam\’iyyar ga shiyyarsu ba.
  An dai cimma wannan kudurin ne a yayin taron majalisar zartarwar jam\’iyyar karo na 70
  da aka yi ranar Alhamis.
  A watan Mayu ne dai jam\’iyyar ke shirin gudanar da babban taronta na kasa domin
  zabar sababbin shugabanni.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here