AN KAMA BARAYIN DA SUKA KASHE WANI ALMAJIRI YAYIN YIN SATA

0
1124

Daga Usman Nasidi

DUBUN wadansu barayi da ake zargi da kashe wani almajiri lokacin da suka je sata ta cika,
bayan da aka kama jagoransu da ake kira Na- Turunku da ke zaune a Jushi, Zariya a Jihar Kaduna.
Ana zargin Na-Turunku da yin kaurin suna wajen kisa da sata da kuma kwace, kuma saboda mugun ta’addancin da ake zarginsa ne mutanen garejin da yake aiki da jama’ar unguwa suka yi masa iyaka da garejin a bayan Asibitin Musulmi a Tsohuwar Kasuwa Danmagaji, Zariya.
A ranar Asabar da ta gabata ne maigadin garejin mai suna Abubakar ya kai almajirin mai suna Muhammadu zuwa wurin masu garejin domin su ba shi hayar kurar daukar ruwa ya fara sana’a, amma sai suka ce su koma sai ranar Lahadi da karfe 11:00 na safe domin su je wurin malamin almajirin kafin su ba shi hayar kurar.
Bayanai sun ce Abubakar Maigadi ya bukaci almajiri Muhammadu ya tsaya su kwana a wurin gadin, daga baya ya tafi gida ya bar almajirin ya kwana. An ce cikin daren almajirin na kwance sai barayin suka zo suka tarar da shi yana barci suka far masa da sara da suka suka kashe shi, suka dauki gawarsa suka sanya a motar wani makwabcin wurin mai suna Musa,
wanda ya kai ajiyar motarsa garejin kan zai yi sammako washegari. Kuma daga nan ne barayin suka fasa wani shago suka kwashe alminiyon da aka kiyasta kudinsa a kan Naira dubu 100.
Sai dai kuma ’yan banga sun kama Na-Turunku da kayan da suke zargin na sata ne kuma suna cikin bincike ne sai ga wasu daga cikin kayan da aka sace a garejin da aka kashe almajirin.
Na-Turunku ya bayyana wa wadanda suka kama shi cewa ba shi kadai ya yi kisa da satar ba, abokan yin sa suna zaune a kauyen Dogon- Dawa da ke hanyar Birnin Gwari, kuma bayan
yin aika -aikar sun koma inda suke.
’Yan bangar sun sanar da ’yan sanda halin da ake ciki tare da mika shi gare su domin su ci gaba da bincike.
Da wakilinmu ya tuntubi malamin almajirin, ya ce ba zai ce komai a kan lamarin ba, sai makusantan marigayi Muhammadu sun zo kafin su dauki matakin da ya kamata.
Babban Jami’in ’Yan sanda (DPO) mai kula da yankin Danmagaji Kassim Abdul ya tabbatar da
kisan almajirin tare da kama Na-Turunku da abokan zarginsa biyu, kuma ya ce sun tura su
sashin binciken manyan laifuffuka na rundunarsu da ke Kaduna domin ci gaba da bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here