Mahara Sun Kashe Mutane 10 A Jihar Zamfara

0
1155

Imrana Abdullahi Daga Kaduna

Wadansu mutanen da ake zargin cewa Filani ne sun kai hari a wasu kauyuka biyu cikin Jihar Zamfara.

Maharan da ake kyautata zaton cewa Fulani ne sun kai harin ne a kan Barura kusan Sittin a kauyen Badada suka kashe mutane 7 sai kuma a kauyen Ruwan Tofa suka kashe mutane Uku tare da jikkata wasu sakamakon raunukan da suka yi masu.

Bisa faruwar irin wadannan kai hare haren ne ma yasa shugaba Buhari bayar da umarnin dubawa tare da daukar matakan da suka dace domin magance faruwar hakan.

Sai  dai mun yi kokarin jin ta bakin jami\’an tsaro amma lamarin ya ci tura domin hakarmu ta kasa cimma Ruwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here