Ya Nemi A Sanya Tsari Wajen Zaben Cike Gurbi

  0
  1037

   

  Jabiru A Hassan, Daga  Kano.
  AN bayyana cewa rashin kyakkyawan tsari shi ne ya jawo rikicin da ya faru a zaben cike gurbi na dan majalisar dokoki a karamar hukumar Minjibir.
  Wani tsohon dan majalisa a jamhuriya ta biyu, Alhaji  Amadu Abdullahi sh ine ya sanar da haka a wata zantawar su da gaskiya Ta Fi Kwabo, inda ya kara da cewa  dole ne a rika samun hargitsi a zaben cike gurabe musamman saboda yadda ake barin kowa yana zuwa wajen zabe a duk lokacin da za a yi shi.
  Sannan ya nunar da cewa yana da kyau a rika barin \’yan gida su kadai su rika yin zaben suna cike gurbi maimakon a rika tura kowa zuwa wajen zabe wanda a cewarsa hakan ko kadan ba daidai ba ne.
  Alhaji Amadu Abdullahi ya kuma bayyana cewa abubuwan da suka faru a karamar hukumar Minjibir babu dadi ko kadan, don haka wajibi ne a yi shiri mai kyau da gamsarwa a duk lokacin da  aka sanya wata sabuwar rana ta yadda za a yi zabe cikin kwanciyar hankali.

   

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here