An Yi Jana\’izar Hazikan Daliban Jihar Kano Su 8

0
1137

Jabiru A Hassan, Daga Kano.

AN yi jana\’izar daliban Jihar Kano 8 da suka rasu sanadiyyar hadarin motar da ya rutsa da su yayin da suke dawowa daga wata gasa  wadda aka gudanar a Jihar Legas da safiyar jiya Alhamis 5 ga Mayu  a makabartar Tarauni da ke Birnin Kano.
Daliban wadanda suka wakilci Jihar Kano, sun fito ne daga makarantu guda biyu  kuma  sun yi hadarin ne sanadiyyar fashewar tayar motar da suke ciki  kuma  direban motar da wani jami\’i wanda ya kula da gasar su ma sun rasu.
Haka kuma akwai dalibai 3 da a halin yanzu suke asibiti suna samun kulawa kamar yadda Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarni, sannan ya gana da iyayen yaran tare da yi  masu ta\’aziyya  a wani zama da ya yi da su a gidan gwamnati, kuma ana ci gaba da karbar gaisuwa daga al\’umma bisa wannan babban rashi da Jihar Kano da ma kasar Najeriya ta yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here