Dan majalisar dokokin Filato mai wakiltar Jos ya tallafa wa Makarantun Ittahadu

  0
  1063

  Isah Ahmed Daga Jos

  DAN majalisar dokokin Jihar Filato mai wakiltar mazabar Jos ta arewa
  maso arewa Alhaji  Ibrahim Baba Hassan ya tallafa wa daliban makarantun
  kungiyar malaman makarantun islamiya ta Jihar Filato [ Ittihadu
  Anwaril Hidayat] da Unifom.
  Da yake mika wannan tallafi ga shugaban kungiyar ta Ittihadu Anwaril
  Hidayat Alhaji Yusuf Yahaya a wajen taron tunawa da ranar Isra\’i da
  Mi\’irajin Manzon Allah SAW da kungiyar ta shirya a garin Jos, Alhaji
  Ibrahim Baba Hassan ya yi  fatar wannan tallafin  unifom da ya  bayar
  zai kara karfafawa daliban da suka samu gwiwa kan karatun da suke yi.
  Dan majalisar wanda Alhaji Muhammad Shitu ya wakilta ya yi  kira ga
  daliban  kan su kara zage damtse wajen neman ilmi  domin da ilmi ne
  duniya take ci gaba.
  \’\’Mu kara tashi tsaye wajen neman ilmin addini da ilmin boko. Idan
  muka sami ilmi za mu taimaki kawunanmu da mutanenmu da kasa baki
  daya\’\’.
  Daga nan ya bayar da tabbacin cewa da  yardar Allah zai ci gaba da
  taimaka wa matasan wannan mazaba wajen neman ilmi.
  A nasa jawabin babban limamin Jos Sheikh Lawal Adam ya yi  addu\’ar
  fatar alheri ga  dan majalisa kan wannan tallafi da ya bai wa daliban
  makarantun wannan kungiya.
  Har\’ila yau ya yi  addu\’ar Allah ya kara daukaka wannan kungiya da
  makarantunta da dalibansu baki daya.
  Babban limamin na Jos wanda Na\’ibinsa Sheikh Gazali Isma\’ila Adam ya
  wakilta ya bayyana mahimmanci Isra\’i da Mi\’irajin Manzon Allah SAW. Ya
  ce Sahabban Manzon Allah SAW guda 25 ne suka rawaito Hadisan wannan
  tafiya ta Isra\’i  da Mi\’irajin Manzon Allah SAW saboda mahimmancinta.
  Tun da farko a nasa jawabin shugaban kungiyar ta Ittihadu Anwaril
  Hidayat Alhaji Yusuf Yahaya ya bayyana cewa a bikin Maulidi na
  shekaru uku da suka gabata ne, dan majalisar ya yi masu alkawari na
  ba su wannan tallafi na Unifom. Don haka ya mika godiyarsu ga dan
  majalisar kan wannan alkawari da ya cika masu.
  Ya ce wannan kungiya ita ce take shirya maulidi a garin Jos kuma a
  yanzu ta kirkiro da gasar karatun Hadisai da gasar kasida da taron
  Muharram da kuma  taron tunawa da Isra\’i da Mi\’irajin Manzon Allah.
  \’\’Shi musulmi a rayuwarsa  babu abin da yake kauna kamar Annabi
  Muhammad SAW don haka  kungiyar nan, ta kirkiro da wannan taro na
  tunawa da ranar Isra\’i da Mi\’irajin Annabi Muhammad SAW. Ya zama
  wajibi musulmi su rika girmama wannan rana ta 27 ga watan Rajab wato
  ranar da Manzon Allah Annabi Muhammad SAW ya yi Isra\’i da Mi\’iraji
  saboda mahimmancinta\’\’.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here