Buhari Bai Ji Dadin Kalaman David Cameron Ba

0
1136

Imrana Abdullahi Daga Kaduna

SHUGABAN Najeriya da Talakawan kasar suka zaba da gagarumin rinjaye Muhammadu Buhari, ya bayyana matukar damuwarsa da kalaman Firayim ministan Ingila David Cameron da ya bayyana Najeriya da Afghanistan da cewa sun fi kowace kasa matsalar cin hanci da rashawa.

Shi dai David Cameron ya fadi hakan ne lokacin da ya kaiwa sarauniyar Ingila ziyara tare da rakiyar shugaban majalisa da kuma wasu kusoshin gwamnatinsa.

An dai ji Cameron na yin rada ne cewa za a yi wani taro a kan cin hanci da karbar rashawa kuma wasu kashe biyu da suka fi fama da wannan matsalar za su halarta, ya kuma bayyana a cikin radar tasa cewa Najeriya da Afghanistan ne kasashen.

Amma bisa bayanan da suke fitowa a halin yanzu na bayanin cewa shugaba Muhammadu Buhari na cewa bai ji dadin wadannan kalaman ba da suka fita daga bakin Cameron musamman kamar yadda jaridun intanet suka rika radawa duniya a cikin dan karamin lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here