NAKASASSU SUN BA EL -RUFA\’I WA\’ADIN KWANA 5 YA JANYE DOKAR HANA BARA

0
1357

 

IMRANA ABDULLAHI Daga Kaduna

KUNGIYAR Nakasassu ta kasa reshen jihar Kaduna sun ba Gwamnan Jihar Mal. Nasir Ahmed El-rufai wa\’adin kwana biyar da ya gaggauta janye dokar hana bara da ya sanya wa hannu.

In ba a manta ba kwanan baya ne gwamnan ya tura yan majalisar jihar
kudirin hana bara da talla a jihar inda daga bisani yan majalisr suka
kaddamar da kudirn ya zama doka gwamnan kuma ya sa mata hannu ta zama
doka.

A saboda sa hannun da gwamnan ya yi kudirin ya zama doka, Naksassun
suka   gudanar da zanga-zanga ta lumana yau Laraba inda suka bai wa
Gwamna Nasir Ahmed El-rufai wa\’adin kwana biyar da ya janye wannan doka.

 

 

\"IMG_20160511_114045\"

Da yake jawabi a chibiyar yan jarida reshen jihar Kaduna Mai magana da
yawun kungiyar Kwamarde Lurwanu Abdullahi yace, \” ranar litinin mai
zuwa zamu kara yin wata zanga- zangar a fadar gidan gwamnatin jihar ,
ko muyi rai ko kar muyi zamu hallara kwanmu da kwarkwatar mu don nuna
bacin ran mu akan wannan doka.\”

Ya ce, \”El-rufai ya yaudare mu domin lokacin yakin zaben sa naa gwamna
ya yi mana alkawari cewar bazai yi dokar da zata takurawa rayuwar mu
amma abin takaichi ashe yaudara ce yayi mana.\”

 

 

 

\"IMG_20160511_113419\"

Kwamared Lurwanu yayi nuni da cewar\” dole ce tasa muke yin bara ba
akan san ranmu kuma muna yi ne don kare hakkin iyalan mu.\”

Nakasassun sun gudanar da zanga- zangar ne a sakatariyar yan jarida
reshen jihar kaduna inda suke dauke da takardu da aka rubuta kamar
haka; yan majalisar jihar Kaduna sunchi amanar mu, a bamu kashi dari
na aikin yi kafin a hana bara, a kaddamar da kudirin mu na kirkiro
mana da hukumar nakasassu da shauran su.

# Ba Zamu Daina Bara Ba Sai Dai A Kashe Mu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here