Kotu Ta Hana NLC Shiga Yajin Aiki

0
1026

Rabo Haladu Daga Kaduna

KOTUN sasanta \’yan kwadago ta dakatar da kungiyar kwadago NLC
tafiya yajin aikin da take shirin farawa ranar Laraba.
Ministan shari\’a  Barista Abubakar Malami wanda ya tabbatar wa da manema  labarai  hakan, ya ce kotun ta yi hakan ne domin hana fadawar kasar cikin halin ni-\’ya-su.
Sai dai kuma ministan ya ce dakatarwar ta wucin-gadi ce kuma gwamnati na ci gaba da
tattaunawa da kungiyar ta kwadago.
Kungiyar kwadagon dai ta ba wa gwamnatin zuwa karfe 12 na daren Talata da ta
janye karin farashin mai da ta yi daga N86 zuwa N145, ko kuma ta tafi yajin-aikin sai illa-
Ma Sha-Allahu.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here